Hukumomin kasar sun ce jami'an tsaro sun hallaka daya daga cikin 'yan bindigar, yayinda kuma ake farautar dayan.
Harin ya faru ne a birnin Sousse, inda baki 'yan yawon bude ido da dama daga kasashen Turai da arewacin Afirka ke tururuwar zuwa.
Karo na biyu kenan ana kai harin a wurin 'yan yawon bude ido a kasar ta Tunisia.
A cikin watan Mayu ma, harin 'yan bindigar ya hallaka mutane fiye da 20 a gidan ajiye kayan tarihi na Bardo da ke Tunis, babban birnin kasar.288